Cibiyar dakile bazuwar cututtuka ta kasa NCDC a jiya ta tabbatar da cewa kimanin mutane 6 ne suka mutu sanadiyyar cutar corona.

NCDC ta bayyana hakan ne cikin sakonnin da take wallafawa a kowacce rana, haka kuma hukumar tace a jiyan ansamu sabbin mutane 537 da suka kamu da cutar.

An kuma samu sabbin mutanen ne a Jihohin kasar nan 7 ciki harda babban birnin tarayya Abuja.

Da wannan sabbin adadin yanzu haka dai kimanin mutane dubu dari 248 da dari 997 ne suka kamu da wannan cutar tun bayan bullarta a kasar nan a watan Janairu na 2020.

Haka kuma kimanin mutane dubu dari 218 da 997 ne aka sallamesu bayan sun warke daga cutar.

Sai kuma mutane dubu 3 da 77 da suka mutu dalilin cutar a cikin Jihohin kasar nan 36 da babban birnin tarayya Abuja.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: