Mutum 9 sun rasu, 50 sun samu raunika a wani hadarin mota da ya faru a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa

0 59

Hukumar Hana Afkuwar Hadura ta Kasa reshen Jihar Jigawa ta ce kimanin mutum 9 ne suka rasu, yayin da wasu mutane 50 suka samu raunika a wani hadarin Mota da ya faru a karamar hukumar Ringim ta Jihar nan a jiya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa Kakakin Hukumar Malam Ibrahim Gambo, shine ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce lamarin ya faru ne a kan hanyar Chai-Chai zuwa Kwanar Shafar.

Malam Gambo ya ce an fadawa Ofishin su faruwar lamarin da misalign karfe 6:23 na Dare, inda suka tura Jami’an su zuwa wurin tare da kaiwa wanda suka samu raunika zuwa Asibitin Ringim domin samun kulawar likitoci.

Haka kuma ya ce kimanin mutane 70 hadarin ya rutsa da su, a wata Motar DAF wanda wani mai suna Babangida Muhammad ya ke tukawa.

Kazalika, ya dora alhakin faruwar lamarin kan gudunwuce sa’a da karya ka’idojin tuki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: