Rundunar Sojin Saman Najeriya sun kashe yan bindiga 50 a Jihar Zamfara tare da hallaka wasu 33 a Jihar Kaduna.

Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa sabbin hare-haren da Jiragen sojojin saman suka kai a Dajin Sangeko na Zamfara da sabuwar Kasuwa a Kaduna, ya yi sanadiyar mutuwar yan bindigar da dama.

An rawaito cewa rundunar Operation Hadarin Daji ne ta kaddamar da hare-haren a lokacin da daya daga cikin Jiragen ta ya hango yan bindigar su kimanin 50 akan Baburan su cikin Dajin Sangeko na karamar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

Jirgin ya hallaka 33 daga cikin yan bindigar bayan ya hango su, kamar yadda wata Majiya ta fadawa Jaridar PRNigeria ta wayar tarho.

Wani bincike da PRNigeria ta yi a Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa Sojojin sun gudanar da wasu hare-haren a ranar 30 da 31 ga watan Maris a Kusasu.

Jirgin Sojojin ya hangi Babura 4 na yan fashin Daji a cikin Daji Kusasu.

Kakakin Rundunar Sojin Saman Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da labarin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: