Sojojin haya ne zasu iya magance matsalar tsaro a Najeriya – Gwamna El-Rufa’i

0 71

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya yi barazanar cewa shi da sauran gwamnonin yankin Arewa za su ɗauki sojojin haya don kare rayukan mutanensu idan gwamnatin tarayya ta kasa kawo ƙarshen hare-haren ‘yan fashi a yankin.

Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ya gana da shugaba Buhari a jiya Juma’a, El-Rufai ya ce ba ‘yan fashin daji ne suka kai hari kan jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja ba yan Boko Haram ne.

Gwamnan wanda ya yi Jawabi da Hausa, ya ce karuwar matsalolin tsaro a Kaduna, wanda yunkuri ne na durkushewar tattalin arzikin Jihar dama Arewacin kasar.

A ranar Litinin ne yan bindigar suka kai hari kan Jirgin Kasar Abuja zuwa Kaduna, a kusa da Kateri-Rijana.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce Fasinjoji 362 ne suka hau Jirgin, inda 26 daga cikin su suka raunata, baya ga mutum 8 da yan bindigar suka kashe a lokacin.

El-Rufai, ya bayyana cewa Maharan suna son lalata babban zaben shekarar 2023 da ke tafe a kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: