Najeriya ta tara $500M domin inganta tsarin samar da abinci

0 270

Mataimakin shugaban kasa Kashin Shettima ya bayyana cewa Najeriya ta tara kimanin rabin dala bilyan daya, domin samar da sabbin tsare-tsare masu riba, a yunkurin samar da tsari mai dorewa a bangaran abinci.

Daraktan yada labarai na ofishin mataimakin shugaban kasa Olusola Abiola a cikin wata sanarwa da ya fitar, yace Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar wani babban taro kan tsarin samar da abinci a birnin Rome na kasar Italiya.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, an tattara kudaden ne ta hanyar albarkatun cikin gida, bankunan raya kasashe da, cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa da da asusun sauyin yanayi da kasuwancin noma

Ya ce za a yi amfani da kudaden ne wajen samar da canjin tsarin abinci, darajar noma a Najeriya da kuma kafa yankunan sarrafa masana’antu na musamman.

Tun da farko, yayin da yake  bude taron, babban sakatare na majalisar dinkin duniya Guteress, ya yabawa kasashen da suka halarci taron, bisa jajircewarsu na magance matsalolin yunwa da rashin abinci mai gina jiki. Mataimakin shugaban kasa ya kuma gana da firaministan Italiya Giorgia Meloni, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban kasashen biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: