PDP ta roki kasashen duniyA da su titsiye Shugaba Buhari akan matsalar tsaro a Najeriya

0 98

Jam’iyyar PDP ta roki kasashen duniya da sauran hukumomin dimokuradiyya da su tambayi Shugaba Muhammadu Buhari kan rawar da gwamnatinsa ke takawa wajen karuwar ta’addanci, da take hakkin dan adam, da magudin zabe, da cin hanci da rashawa, da rabuwar kawunan ‘yan kasa, da rugujewar tattalin arzikin kasa cikin shekaru shida da suka gabata.

Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi a zaman majalisar dinkin duniya karo na 76 a birnin New York a gobe.

PDP, a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar a yau, ya ce tsarkin rayuwar dan adam, da ‘yanci, da mutunta ‘yancin dan adam, da adalci da bin doka, da zabe mai inganci, da gudanar da mulkin dimokradiyya, da inganta zaman lafiya, da rikon amana a harkokin mulki, da bunkasa tattalin arziki da sauransu, wanda zauren majalisar dinkin duniya ya tsaya a kai duk gwamnatin Buhari ta keta su.

Ya ce baya ga wadannan, akwai rashin biyayya ga umarnin kotu, da amfani da jami’an tsaro don murkushe ‘yan kasa, da cin zarafin kafofin watsa labarai, da rashin adalci na tsarin da ke nuna halin da ake ciki a Najeriya karkashin mulkin Buhari, kamar yadda kotun manyan laifuka ta duniya ta bayyana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: