A wani Labarin kuma, Babbar jam’iyyar hamayya ta Kasa wato PDP ta yi Allah-wadai da abin da ta kira murƙushewar da jami’an tsaro ke yi wa ‘yan Najeriya masu zanga-zangar lumana a Ranar Dimokuraɗiyya.

Da safiyar yau ne masu zanga-zanga suka hau kan tituna musamman a jihohin kudu domin nuna damuwarsu game da halin da Najeriya ke ciki a yankunansu.

Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun kama mutane da dama a Legas da Abuja tare da harba musu hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa su sai dai daga baya sun saki wasu daga cikin su.

Cikin wata Sanarwa da PDP ta fitar kuma aka rabawa manema labarai, PDP ta kwatanta murƙushewar da ake yi wa ‘yan ƙasa a matsayin cin zarafin dimokuraɗiyya da jam’iyyar APC ke yi da kuma wulaƙanta ‘yan Najeriya musamman a lokacin da suke neman haƙƙinsu.

Haka kuma, Jam’iyyar ta nemi a kawo ƙarshen Karya kundin tsarin mulki sannan ta yi kira ga ƙasashen duniya da lura da abin da gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke aikatawa “na take haƙƙin ɗan Adam”.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: