Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta cafke wani mutum bisa satar motar daukar marasa lafiya

0 96

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wani mutum mai shekaru 40 da haihuwa bisa zargin satar motar daukar marasa lafiya ta karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar jiya a Dutse.

Shiisu Adam ya ce an kama wanda ake zargin ne a kauyen Takwasa da ke karamar hukumar Babura a jiharnan.

Ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne bayan da ‘yan sanda suka samu rahoton cewa an sace motar daukar marasa lafiya a kauyen Kanya Hore da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan ya ce ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin bayan an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: