Rundunar hadin gwiwa ta kasa-da-kasa ta gano wata kasuwar kifi ta boye da mayakan Boko Haram dana ISWAP

0 106

Rundunar hadin gwiwa ta kasa-da-kasa ta gano wata kasuwar kifi ta boye da mayakan Boko Haram dana ISWAP suke mu’amala da ita dake yammacin Afirka a gabar tekun tafkin Chadi.

Rundunar ta kara da cewa an kama mutane a kalla 30 wadanda  masunta ne da manoma a kasuwar.

A cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labaran soji, N’Djamena dake kasar Chadi Lautanal Kanal Kamarudeen Adegoke ya fitar, ya ce sojojin sun bankado tare da kama su a yayin wani samame da suka kai a tafkin Chadi tsakanin ranakun 17 zuwa 21 ga watan Mayu.

Ya kara da cewa, an lalata matsugunan Yan ta’adda 12 a wurare daban-daban a tsawon lokacin da suka gudanar da aikin.

Ya kuma ce sojojin sun kubutar da wata yarinya ‘yar shekara 12 tare da kwato babura, da wata mota kirar Hilux Toyota da dai sauran su.

A wani samame na daban da suka kai a garuruwan Ali Jimari, Dogon Chuku, da Tunbum Rago dake kusa da Tafkin Chadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: