Labarai

Rundunar Tsaro ta Civil Defence reshen jihar Jigawa ta kama wani mutum wanda ya shahara wajen lalata wayar lantarki a karamar hukumar Babura

Rundunar Tsaro ta Farin Kaya wato Civil Defence reshen Jihar Jigawa ta kama wani mutum wanda ya shahara wajen lalata wayar lantarki a karamar hukumar Babura ta Jihar nan.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar CSC Adamu Shehu, ya fitar wanda aka rabawa manema labarai a Dutse.

A cewarsa Jami’an hukumar sun yi nasarar kama Buhari Iliya, dan kyauyen Giginya, a garin Kanya Babba da ke karamar hukumar Babura a jiya Juma’a.

Mutumin ya amince da laifin da ake zargin sa dashi na sa ce wayar lantarkin wata Makaranta har sau biyu.

Binciken da hukumar ta gudanar ya bayyana cewa sun yi nasarar kama wani mai suna Nasiru Shu’aibu wanda shine ya ke siyan kayan.

Hukumar ta ce za’a gabatar da mutanen a gaban Kotu domin girbar abinda suka shuka.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: