Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 36 a wasu hadurran motoci daban-daban a jihar

0 61

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 36 a wasu hadurran motoci daban-daban a jiharnan.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Lawan Shiisu Adam, wacce ya rabawa manema labarai a Dutse babban birnin jiha.

Shiisu Adam ya ce hadurran sun auku ne a cikin watan Fabrairu.

Sawaba ta ruwaito cewa a makon da ya gabata mutane tara ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin da ya ritsa da wata mota kirar Volkswagen Golf Three da keke napep a karamar hukumar Birniwa.

Shiisu Adam ya bayyana cewa wadanda suka rasa rayukansu sun hada da maza da mata da kananan yara.

Ya kara da cewa an yi asarar dukiyoyin miliyoyin Naira a hadurran.

A saboda haka rundunar ‘yan sandan ta gargadi direbobin da su yi taka-tsan-tsan wajen tuki tare da kaucewa gudun wuce gona da iri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: