Labarai

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da cafke wani Kansila dauke da bindiga samfurin AK-47 da harsasai a karamar hukumar Soba

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da cafke wani kansila dauke da bindiga samfurin AK-47 da harsasai a karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Muhammad Jalige ya fitar yau a Kaduna.

Ya ce binciken farko-farko da aka gudanar ya gano bayanin wanda ake zargin wanda kamsila ne mai ci a karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna.

Mohammed Jalige ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Yekini Ayoku, ya yaba da kwazon da jami’an suka nuna kuma yana cike da mamakin dangane da matsayin wanda aka kama.

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan ya bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da cafke duk wadanda ke da alaka da wannan aika-aikar domin fuskantar shari’a.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: