Sama da magoya bayan jam’iyyar PDP da SDP 500 ne suka canja sheka zuwa jam’iyyar APC a Mazabar Gamsarka dake karamar hukumar Auyo

0 90

Sama da magoya bayan jam’iyyar PDP da SDP 500 ne suka canja sheka zuwa jam’iyya mai mulki ta APC a Mazabar Gamsarka dake karamar hukumar Auyo.

Shugaban mazabar, Sale Muhammad Ganuwa ne ya bayyana hakan ayayin da yake jawabi ga magoya bayansa a hekwatar ta Gamsarka.

Shugaban yayi maraba da masu canja shekar ya kuma yi alkawarin yin tafiyar tare da su domin cigaban jam’iyyar.

Ya kuma baiwa sabin mambobin tabbacin yin adalci.

Da yake jawabi, Jagoran masu canja shekar, Muhammad Umar yace sun yanke hukuncin komawa jam’iyyar ta APC ne saboda kyakkyawan tsari da kuma shirye-shiryenta.

Ya kuma yi alkawarin yin aiki rtkuru domin ganin cigaban jami’iyyar a babban zaben 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: