Samfurin shinkafar kasashen waje, musamman na kasashen Thailand da India sun fara mamaye wasu kasuwanni a jihohin Jigawa, Kano da Katsina.
A cewar masana aikin gona da wasu manoman shinkafa, Lamarin mai cike da damuwa ya shafi harkar noma shinkafa sosai a gonaki.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da mutanen da suka shiga harkar noman shinkafa a jihohin Jigawa, Kano da Katsina suke kokawa kan illolin fasa kwaurin shinkafar kasashen waje zuwa kasarnan ta iyakokinta.
An wallafa ra’ayoyinsu a wani rahoto na musamman na wata mujalla.
A wani kokarin habaka noman shinkafa a cikin kasa da kara mata daraja, gwamnatin tarayya a watan Augustan 2019 ta bayar da umarnin rufe iyakokin kasarnan tare da haramta shigowa da shinkafar kasashen waje.
Amma wani bincike da mujallar ta gudanar ya nuna cewa har yanzu shinkafar kasashen waje na cigaba da mamaye kasuwanni dayawa, lamarin dake karya darajar shinkafar da ake nomawa a cikin kasa.