Shirin ACRESAL zai samar da ruwansha mai amfani da hasken rana a jihar Jigawa

0 108

Shirin ACRESAL na jihar Jigawa zai samar da ruwansha mai amfani da hasken rana a was hedikwatocin kananan hukumomin jihar nan uku.

Shugaban shirin na jiha , Alhaji Yahaya Muhammad Ubah Kafin Gana, ya sanar da hakan a lokacin kaddamar da shirin dashen itatuwa da kungiyar daliban Kafin Gana ta shirya.

Ya ce hakan na daga cikin kudirin shirin na gudanar da aiyukan jinkai ga alumma.

Alhaji Yahaya Muhammad Ubah kafingana, yana mai cdwar za a gudanar da aikin ne a hedikwatocin kananan hukumomin Birnin Kudu da Hadejia da kuma Gumel.

Ya bukaci matasa dasu rungumi shirin raya alumma na shirin domin inganta rayuwarsu, tare da yabawa kungiyar daliban bisa gudanar da wannan aiki

A jawabinsa shugaban kungiyar daliban Abubakar Isa ya ce zasu dasa bishiyoyi dubu biyu a makarantu da masalatai da asibitoci da sauran muhimman wurare

Babban Limamin masalacin juma-a na Izala na Kafin Gana Ustaz Ahmed, da Dattijo Saduku Abdul Kafingana sun gabatar da laccoci kan muhimmancin dasa itatuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: