Shugaba Buhari ya buƙaci jami’an tsaron ƙasar nan akan su guji shiga siyasa domin samun nasarar ayyukansu

0 158

Shugaban kasa Muhammadu da ministan tsaro na kasa Bashir Salihi Magashi mai ritaya, sun bukaci jami’an tsaron kasar nan akan su guji shiga siyasa, domin samun nasarar ayyukansu, tare da kare rayukan al’umma, wajan yin biyayya ga dukkan aikin soji.

Shugaban kasar ya bayyana hakan a wurin taron shugaban sojin na kasa da ake gudanarwa a kowacce shekara.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne, ta bakin shugaban dakarun tsaron kasar nan General Lucky Irabor wanda yayi magana a madadinsa.

Inda ya kara da cewa, domin dorewar demokiradiyya dole ne sai an tabbatar an kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kara da cewa dole ne jami’an tsaro su barranta kan su daga shiga fannonin siyasa da kabilanci.

Anasa bangaren shugaban sojin kasar nan Faruk Yahaya ya bayyana cewa jami’ansu a shirye suke, su kare demokiradiyya da kuma martabar kasar nan baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: