Kamar yadda BBCHausa suka wallafa a shafin su:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin dage haramcin amfani da Twitter a kasar, amma in kamfanin ya cika sharudan da aka gindaya masa.

Har zuwa safiyar Juma’a akwai wannan haramci, duk da cewa shugaban kasar ya ce ‘yan kasar za su ci gaba da amfani da manhajar a matsayin “hanyar kasuwanci da kuma ci gaban rayuwa”.

A bayanin da ya yi na ranar samun ‘yanci ya ce, tawagar shugaban kasa ta tattauna da wakilan kamfanijn Twitter a lokuta da yawa kan batutuwa masu yawa da suka kama daga na matsalar tsaro da na haraji da dai sauransu.

Har yanzu dai kamfanin Twitter bai ce komai kan kalaman shugaban.

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da ayyukan Twitter a watan Yuni bayan bayan shafin ya goge wasu sakwanni da shugaban ya wallafa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: