Wani mashahurin jagoran yan fashin daji ya mayar da helkwatasa daga jihar Zamfara zuwa Sokoto

0 134

Wani mashahurin jagoran yan fashin daji mai suna Muhammad Bello, wanda aka fi sani da Turji, ya mayar da helkwatasa daga Fakai a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, zuwa gabashin karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Wasu majiyoyi wadanda suka zanta da manema labarai sun ce mai yiwuwa Turji ya gujewa hare-haren da sojoji ke shirin kaddamarwa bisa umarnin gwamnatin jihar Zamfara.

Matashin mai shekaru 27 dan fashi ne mara tausayi da ke aiki a jihoshin Sokoto da Zamfara. A lokuta da dama, ya ki amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya daga gwamnatocin jihoshi.

Lokaci guda da ya ce yana da bukatar tattaunawa shine lokacin da malamin addinin musulunci jihar mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi, ya ziyarci sansaninsa da ke Zurmi a Jihar Zamfara.

Turji ya kasance yana rike da mahaifi da kaka da kawun kakakin majalisar dokokin jihar, Nasir Magarya, wanda ya yi garkuwa da su tare da wasu mutanen, kimanin watanni biyu da suka gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: