Shugaban Hukumar ICPC Farfesa Bolaji, Ya Bayyana Cin Hanci Da Rashawa A Matsayin Babbar Matsala Wacce Dole Matasa Su Yake Ta
Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran laifuka masu alaka, ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya bayyana cin hanci da rashawa a matsayin Babbar matsala wacce dole matasa su yake ta.
Shugaban wanda ya samu wakilcin Alli Goni Gujba, wakili a hukumar ta ICPC, ya bayyana haka ne jiya a Abuja, a wajen taron muhawarar farko da hukumar ta gudanar tsakanin manyan makarantun babban birnin tarayya da na jihar Nasarawa.
Shugaban hukumar ta ICPC ya bayyana matasa a matsayin manyan gobe, wadanda ke da bukatar yaki da cin hanci da rashawa da tsauri domin cimma burin da ake so.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bukaci matasan da su ba da tasu gudummawar ga Nijeriya wajen kawo karshen laifukan tattalin arziki da kudade. Abdulrasheed Bawa, wanda Chidimma Amanambu, mataimakin kwamandan EFCC ya wakilta, ya hore su dasu ba da tasu gudummawar domin kawo karshen cin hanci da rashawa.