Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabbin manyan daraktoci guda 6

0 162

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabbin manyan daraktoci guda 6 na  ma’aikatar kula da harkokin ruwa da tattalin arzikin kasa ta kasa

A cewar mai magana da yawun shugaban kasa Ajuri Ngelale, shugaban kasa ya nada sabbin manyan daraktoci guda uku na hukumar kula da jiragen ruwa da hukumar kula da tabbatar da tsaro ta gabat tekun kasar nan NIMASA.

Shugaban kasar ya nada Vivian Edet a matsayin babban daraktar mai kula da sha’anin kudi da mulki na hukumar kula da jiragen ruwa ta kasa NPA, da Olalekan Badmus babban daraktar hukumar, sai kuyma Ibrahim Umar a matsayin babban daraktan sashen injiniyanci. A bangaran hukumar kula da samar da tsaro a gabar tekun kasa NIMASA, shugaban kasa ya nada Jibril Abba babban daraktan kula da jirage da ayyuka na hukumar, sai kuma Chudi Offodile daraktan kudi da mulki na hukumar da Fatai Adeyemi daraktan ayyuka na hukumar ta NIMASA

Leave a Reply

%d bloggers like this: