Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Bada Umarnin A Gaggauta Taimakawa Marasa Karfi Domin Dakile Tasirin Cire Tallafin Mai
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci majalisar tattalin arzikin kasa karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da ta fara aiki akan taimakawa marasa karfi domin dakile tasirin cire tallafin mai ga ‘yan Najeriya.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da manyan ‘yan kasuwar mai masu zaman kansu suka yi alkawarin baiwa gwamnatin tarayya gudunmawar manyan motocin bas masu daukar akalla mutane 100 domin gudanar da zirga-zirgar jama’a.
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, wanda ya jagoranci wakilan wasu manyan ‘yan kasuwar man fetur a wata ziyarar ban girma da suka kai wa shugaban kasa Bola Tinubu, ya sanar da wannan labari mai dadi a jiya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan kammala ganawar sirrin, Gwamna Dapo Abiodun ya ce ’yan kasuwar sun kasance a fadar shugaban kasa domin nuna goyon bayansu ga shugaban kasa kan matakin da ya dauka na kawo karshen tallafin man. Ya yi nuni da cewa, matakin na Bola Tinubu ya nuna jajircewarsa da juriyarsa wajen kawar da matsalar da ta addabi kasar nan tsawon shekaru da dama.