Shugaban kasa Buhari ya tashi daga Abuja zuwa kasar Equatorial Guinea domin halartar taron shugabannin kasashen Afrika kan matsalar tsaro

0 113

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau ya tashi daga Abuja zuwa Malabo, babban birnin kasar Equatorial Guinea domin halartar taron shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afrika na musamman wanda zai mayar da hankali akan tsaro.

Shugaban kasar ya samu rakiyar mai dakinsa, Aisha Buhari, da Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, da ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, mai ritaya, da ministar harkokin jin kai, kula da annoba da walwalar jama’a, Sadiya Umar Farouq, da mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno, mai ritaya, da darakta janar na hukumar leken asiri ta kasa, Ambassada Ahmed Rufa’I Abubakar da shuganar hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, cikin wata sanarwa yace taron na wuni uku, wanda za a fara daga yau zuwa jibi, zai kuma mayar da hankali akan kalubalen ayyukan jin kai a Afrika, da matsalolin gudun hijira.

Yace a wajen taron, shugabannin Afrika zai duba matsalar ta’addanci da juyin mulkin da ya sabawa kundin tsarin mulki da kuma matsalolin da yake jawowa na yancin dan adam da tattalin arziki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: