Shugaban kasa Buhari ya yi alhinin mutuwar mutane 141 sanadiyyar ruftawar wata gada a Indiya

0 75

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar mutane 141 sanadiyyar ruftawar wata gada a kasar Indiya.

Yawancin wadanda abin ya shafa, da suka hada da mata, yara, da tsofaffi, sun mutu ne a ranar Lahadi bayan gada ta ruguje a Morbi, kwanaki 6 kachal da gyaranta.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin wata sanarwa a jiya ta bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa da gwamnati da al’ummar Indiya.

Baya ga wadanda suka mutu, an ceto mutane 177 daga cikin 500, kuma hukumomi na neman wasu da dama da suka bace.

Shugaba Buhari ya kuma yi addu’ar samun lafiya ga dukkan mutanen da suka samu raunuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: