Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano da ‘Yan Majalissu 22 Sun Yi mubaya’a ga Gwamna Abba Kabir Yusuf
Shugaban Majalissar Dokokin Jihar Kano, Ismai’l Falgore, mataimakinsa, Muhammad Bello Butu Butu, da wasu ‘yan majalissa 22 sun fita daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), tare da bayyana cikakken goyon bayansu ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Majalissar Dokokin Jihar Kano ta fitar, wadda Sakataren Yada Labarai na Majalissar, Kamaludden Sani Shawai, ya sanya wa hannu.
A cewar sanarwar, daga cikin waɗanda suka fice daga jam’iyyar NNPP tare da gwamnan akwai Shugaban Majalissar, Rt. Hon. Jibril Ismai’l Falgore, Mataimakin Shugaban Majalissar, Rt. Hon. Muhammad Bello Butu Butu, da Shugaban Masu Rinjaye (Majority Leader), Hon. Lawan Hussain.
Haka kuma, an lissafa Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye, Hon. Garba Shehu Fammar, Babban Mai Tsawatarwa (Chief Whip), Hon. Muddasir Ibrahim Zawachiki, tare da wasu ’yan majalissa da ke wakiltar mazabu daban-daban a faɗin jihar.
Sanarwar ta ce jimillar ’yan majalissar shine 22 ne suka shiga wannan sauyin sheƙa, inda suke wakiltar mazabu kamar Ajingi, Albasu, Bagwai/Shanono, Bebeji, Bunkure, Dawakin Kudu, Fagge, Gabasawa, Garko, Gwale, Karaye, Kura/Garun Malam, Madobi, Minjibir, Rano, Tarauni, da Wudil.
Ta ƙara da cewa Majalissar Dokokin Jihar Kano ta bincika tare da tabbatar da sahihancin jerin sunayen ’yan majalissar da aka fitar.
Majalissar ta bayyana cewa an yi wannan sanarwar ne domin sanar da al’umma yadda ya kamata da kuma fayyace matsayar siyasa ta ’yan majalissar da abin ya shafa, bayan sauyin jam’iyyar da gwamnan ya yi.