Sufeto-Janar na ‘yan sandan kasa, Usman Alkali Baba, ya bayar da umarnin a gaggauta rabawa jami’an ‘yansanda kaki da sauran kayan aiki a fadin kasar nan.

Kakakin rundunar yansanda, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai.

A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan, wannan karimcin wani bangare ne na burin Sufeto-Janar na ‘yan sandan na sake farfado da bayar da kakin ‘yansanda da sauran kayan aiki sau hudu a shekara ga masu mukamin sufeto zuwa wadanda ke kasa da su da kuma kurata.

Ya kara da cewa kakin da sauran kayan aikin kyauta ne ga duk wani jami’in ‘yansanda mai mukamin sufeto zuwa kasa kamar yadda aka tanadar a cikin kasafin kudin ‘yan sanda.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: