Sule Lamiɗo Ya Baƙunci Garin Hadejia Don Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Rasuwar Jigogin Yankin da suka Rasu

1 245

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya kawo ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigari Alhaji Garba Danjani Hadejia, wanda ya rasu ranar Litinin da dare, bayan gajeriyar jinya.

Alhaji Sule Lamido ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan Magajin Garin Hadejia, Alhaji Hamisu Ibrahim, bisa rasuwar ‘yarsa.

Haka zalika, tsohon gwamnan, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Marigayi Babangida Muhammad Milo.

Alhaji Sule Lamido, yayi addu’ar Allah SWT ya jikan mamatan, tare da bawa iyalansu hakurin jure rashin.

Daga cikin ‘yan rakiyar tsohon gwamnan, akwai shugaban jam’iyyar PDP na jiha, Alhaji Salisu Mamuda, da tsofaffin ‘yan majalisar dokokin jiha, da kuma dumbin magoya baya.

  1. Muhammad Danasabe says

    Allah yakara Daukaka Gidan Radio Sawaba fm Nagode

Leave a Reply

%d bloggers like this: