Labarai

Taliban ta umurci mata masu gabatar da shirye-shiryen talabijin na Afganistan da sauran matan da ke bayyana a talabijin da su rufe fuskokinsu yayin da ake haska su

Taliban ta umurci mata masu gabatar da shirye-shiryen talabijin na Afganistan da sauran matan da ke bayyana a talabijin da su rufe fuskokinsu yayin da ake haska su.

Wani mai magana da yawun ‘yan Hisbah ya shaidawa manema labarai cewa an shaida wa kafafen yada labarai wannan dokar a ranar Laraba.

Hukuncin dai ya zo ne makonni biyu bayan da aka umarci dukkan mata da su rufe fuskokinsu a bainar jama’a, ko kuma su fuskanci hukunci.

Ana kara tsaurara matakai akan mata bayan hana su tafiye-tafiye ba tare da muharrami ba, sannan kuma an rufe makarantun sakandare na mata.

Wata ‘yar jarida ‘yar kasar Afganistan da ke aiki a wani gidan talabijin na kasar a Kabul babban birnin kasar, wadda ba ta so a bayyana sunanta ba, ta ce ta yi matukar kaduwa da jin sabon labarin.

Kakakin Hisbah ya kira hukuncin a matsayin shawara kuma ba a san abin da zai biyo baya ga duk wanda ya ki bin umurnin ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: