Tuhume-tuhume 32 na sama da fadin da kudin su yakai Naira miliyan 36,000 ake yiwa Saminu Turaki – Kotu

0 71

Babban kotun tarayya dake zama a Dutse ta dage sauraron shari’ar da ake yiwa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sanata Ibrahim Saminu Turaki da wasu mutane 4 bisa zargin sama da fadi da kudi naira miliyan dubu 36, zuwa ranar 31 ga watan Maris.

Sanata Ibrahim Saminu Turaki tare da wasu mutane 4 na fuskantar shari’ah bisa tuhume-tuhume 32 na sama da fadi da da kudi naira miliyan dubu 36. An dakatar da shari’ar shekaru 14 da suka gabata.

Shari’ar da aka shirya dawowa a yau da gobe domin cigaba da sauraro, an sake dage ta zuwa watan na Maris saboda gazawar hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC ta gabatar da sauran wadanda ake zargi a karar.

Kazalika, hukumar ta roki kotun cewa bata shiryawa shari’ar ba.

Sai dai, lauyan Saminu Turaki, Barrista Saidu Muhammad Tudun Wada, yace duk da kasancewar bai soki neman daga shari’ar ba, amma ya nemi a biya shi kudi naira dubu 500 saboda gazawar masu gabatar da kara na sanar da shi akan lokaci cewa basu shirya ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: