Wasu kungiyoyin yan bindiga 2 sun fara kashe akalla mambobinsu a Kaduna

0 67

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa wasu kungiyoyin yan bindiga 2 sun kashe akalla Mambobinsu 9 biyo bayan wani taho mu gama da akayi a tsakanin su.

Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida Mista Samuel Aruwan, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a Kaduna.

A cewarsa, bayanan sirrin da suka samu daga hukumomin tsaro, sun tabbatar da faruwar hakan ga gwamnatin jihar.

Kwamishinan ya ce bayanan sirri sun tabbatar da cewa shugaban yan bindigar mai suna Godon Mota shine ya jagoranci tawagarsa zuwa kyauyen Garke a ranar Laraba, inda sukayi fada tare da wasu mambobin, inda hakan ne ya janyo mutuwar 9 daga cikin su.

Kazalika, Kwamishinan ya ce Mukaddashiyar gwamnan Jihar Kaduna Dr Hadiza Balarabe, ta yabawa kokarin hukumomin tsaro bisa kokarin da suke yi, tare da bukatar su ninka kokarin su.

Samuel Mista Aruwan ya ce ana cigaba da bincike kan faruwar lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: