Wasu shugabanni hudu na jam’iyyar PDP na kasa sun mayar da wasu makudan kudade jumillar naira miliyan 122 da dubu 400 da shugabancin jam’iyyar ya basu.

0 98

Wasu shugabanni hudu na jam’iyyar adawa ta PDP na kasa, sun mayar da wasu makudan kudade jumillar naira miliyan 122 da dubu 400 da shugabancin jam’iyyar ya basu.

An mayar da kudaden ne a daidai lokacin da ake zargin shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, da laifin bai wa shugabannin jam’iyyar na kasa cin hanci, domin su boye maganar badakalar kudi sama da naira miliyan dubu 10 da aka tara daga sayar da fom na tsayawa takara.

Shugabannin jam’iyyar da suka mayar da kudaden sun hada da mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Kudu maso Yamma, Olasoji Adagunodo; da mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa shiyyar Kudu, Taofeek Arapaja; da mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa shiyyar na Kudu maso Kudu, Dan Osi Orbih da; shugabar matan jam’iyyar ta kasa, Stella Affah-Attoe.

An rawaito cewa, Taofeek Arapaja ya samu naira miliyan 36, yayin da Dan Osi Orbih, Stella Effah-Attoe da Olasoji Adagunodo suka samu naira miliyan 28 da dubu 800 kowannensu.

Sai dai a wasu wasiku daban-daban da suka aike wa shugaban jam’iyyar na kasa, shugabannin jam’iyyar sun sanar da shugaban matakin da suka dauka na mayar da kudaden bayan labarin abin kunyar da kafafen yada labarai suka baza.

Leave a Reply

%d bloggers like this: