Malam Abduljabar Kabara da ake tuhuma da laifin yin batanci ya zargi lauyansa da laifin karbar cin hancin Naira miliyan 2

0 122

Malamin addinin musulunci a Kano, Abduljabar Nasir Kabara da ake tuhuma da laifin yin batanci, a jiya ya zargi lauyansa, Dalhatu Shehu-Usman da laifin karbar naira miliyan 2 domin bai wa alkalin babbar kotun shari’a ta Kano cin hanci a ci gaba da shari’arsa.

Ana tuhumar malamin da laifuffuka guda hudu da suka danganci kalaman batanci ga manzon tsira Annabi Muhammad SAW.

Da yake magana da manema labarai bayan zaman kotun, lauyan, Dalhatu Shehu-Usman ya musanta zargin karbar cin hanci.

A wani labarin makamancin wannan daga Kano, wata babbar kotun jihar karkashin jagorancin mai shari’a Sanusi Ma’aji ta dage shari’ar da ake yiwa dan kasar China Geng Quangrong wanda ake zargi da kashe Ummukulthum Buhari a gidansu da ke Kano.

An fara gurfanar da Geng Quanrong ne a gaban kuliya bisa tuhuma guda daya ta kisan kai a gaban Kotun Majistare mai lamba 30, a Sabongari, Kano.

Sai dai a ci gaba da shari’ar a jiya, wanda ake tuhumar ya bayyana ba tare da lauyan da zai kare shi ba, dalilin da yasa alkalin ya dage sauraron shari’ar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: