Wasu yan bindiga sun kai farmaki a mazabar karfi dake karamar hukumar Malumfashi a jihar katsina, an rawaito sun kashe akalla mutane 17.

Wata majiya a yankin ta shaidawa manema labarai cewa yan bindigar kai hari cikin kauyuka akalla 5 duka karkashin mazabar ta Karfi a jiya juma’a, inda suka yi ta Harbin kan mai uwa da wabi kan mutanen kauyukan, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 17 tare da jikkata da dama.

A cewar majiyar yan bindigar sun isa yankunan da misalin karfe 11 na daren jiya juma’a, suka fara harbe-harben tare da sace mutane.

Wani dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar a majalisar dokoki ta jihar Aminu Ibrahim Saidu, wanda ya tabbatar da al’amarin yace ziyarci yankunan da lamarin ya faru domin yin alhini ga iyalan da suka hadu da ibtila’in.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: