Wata kotu a Kano ta tsare wani malami zuwa gidan gyaran hali bisa yi wa dalibarsa mai tabin hankali fyade

0 102

Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Kano a jiya ta bayar da umarnin a tsare wani malami mai suna Sukairaj Kabir mai shekaru 38 a gidan gyaran hali bisa zargin yi wa dalibarsa ‘yar shekara 15 mai tabin hankali fyade.

Kabir wanda ke zaune a unguwar Rimin Auzunawa da ke Kano, ya ki amsa tuhumar da ake masa na aikata laifuka biyu na fyade da kuma cin zarafin yara.

Alkalin kotun, Mustapha Sa’ad-Datti, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Junairu mai zuwa.

Tun da farko dai, lauya mai gabatar da kara, Asma’u Ado, ta shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne tsakanin shekarar 2018 zuwa 2021, a unguwar Tudun Yola da ke Kano.

Asma’u Ado ta ce wanda ake kara, kasancewarsa malamar ajin yarinyar, ya rinka jan hankalinta zuwa wani aji na makarantar Islamiyya, dake unguwar Tudun Yola, Kano.

A cewar lauyar, laifukan sun sabawa tanadin sashe na 283 da 238 na kundin manyan laifuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: