Mamakon ruwan sama da aka tafka a wasu sassa na jihar Jigawa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 a kananan hukumomi 3 na jihar.

Cikin wadanda suka rasa rayukan nasu hadar da wata mata mai dauke da juna biyu da ta mutu sakamakon dannewar da gini ya yi mata yayin da ake tsaka da tafka mamakon ruwan.

Rahotonni sun bayyana cewa iftila’in ya faru ne cikin kwanaki uku inda ake zargin cewa ambaliyar da kogin Hadejia ya yi ce ta haddasa ta inda ta yi sanadiyyar raba fiye da magidanta 600 da matsugunan su sakamakon barnar da ta yi a kananan hukumomi 3 na jihar da suka hadar da  Kirikasamma da Guri da kuma  Birnin Kudu.

Matar mai juna biyu Halima Manu, mai shekaru 35 ta rasu ne tare da ‘ya’yanta biyu Aisha ‘yar shekara 4 da kuma Dauda dan shekara 2 wadanda dukkan su suka mutu sakamakon ruftawar da dakinsu da suke ciki ya yi lokacin da suke tsaka da barci a kauyen Kuradige dake karamar hukumar Kirikasamma.

Su ma wasu ma’aurata Malam Musa Wakili mai shekaru 45 da uwar gidansa Hauwa Musa ‘yar shekaru 35 na daga cikin wadanda rayukan su sakamakon rushewar dakin da suke ciki.

Ita ma wata mata mai suna Fatsima Musa mai shekaru 20 ta rasa ranta sakamakon mamakon Ruwan a garin Auyo da ke karamar hukumar Kafin Hausa.

AUWAL HASSAN FAGGE (WBM)

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: