Yan bindiga sun hallaka shugaban kungiyar Fulani ta MiyettiAllah na kasa Alh Adamu Aliyu a yankin gwagwalada dake birnin tarayya Abuja.

An kashe Aliyu tare da wasu mutane 4 a kusa da kauyen Daku dake mazabar Dobi a ranar alhamis.

Sakataren kungiyar MiyettiAllah na kasa Muhammad Usman wanda ya tabbatarwa da manema labarai da safiyar yau, yace an sace mutane 3 yayin da wasu 3n suka tsira da raunin Harbin bindiga kuma suna karbar kulawar likitoci a asibiti.

Yace lamarin ya farune a ranar alhamis data gabata, lokacin da marigayin shugaban kungiyar na MiyettiAllah da wasu mutane ke kan hanyar dawowa daga kasuwar    Izom a jihar Niger.

Usman yace yan bindigar, wanda suka kewaye dajin tare da bude wuta kan wata mota da take dauke da wadanda lamarin ya rutsa da su.

A rawaito cewa hadakar jami’an tsaro da suka hada da sojoji, jami’an civil depence, yan sanda da yan sa kai sun halarci wajen da lamarin ya auku kafin gudanar da jana’izar mamatan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: