Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Yan Sanda Uku A Jihar Edo

0 81

A jiya ne wasu ‘yan bindiga suka kashe jami’an ‘yan sanda uku yayin da daya kuma ya samu rauni a wani hari da suka kai a jihar Edo.
An tattaro cewa jami’an na zuwa bakin aikinsu ne a lokacin da aka yi musu kwanton bauna a kusa da Agor, kan hanyar Igarra zuwa Auchi a jihar Edo.
An tattaro cewa an kuma kashe daya daga cikin maharan yayin da wani da ya samu raunin harbin bindiga aka kai wani asibiti da ba a bayyana ba domin yi masa magani da kuma yi masa tambayoyi.
An gano cewa an kwato bindigogi shida daga hannun maharan.
An ce ‘yan sandan suna cikin mota ne yayin da wani abokin aikinsu ke kan babur a baya lokacin da aka kai musu hari.
Sai dai dan sandan da ke bin bayansa ya ci karo da maharan wadanda suka gudu cikin daji da bindigun ‘yan sandan hudu bayan kashe su.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, shugaban ’yan banga a yankin, Ibukun Dogo, ya ce sun bi sawun maharan ne ta hanyar tabon jini zuwa maboyarsu inda suka gamu da biyu daga cikinsu da harbin bindiga.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Edo SP Chidi Nwabuzor, ya ce har yanzu rundunar ba ta samu cikakken bayani kan harin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: