Ana fargabar an kashe mutane da dama a jihar Taraba

0 88

Ana fargabar an kashe mutane da dama a wani sabon fada tsakanin Kutafawa da Fulani makiyaya a karamar hukumar Ussa ta jihar Taraba.
Duk da cewa har yanzu ba a san ainihin musabbabin fadan ba, wata majiya ta ce Kutafawa na zargin Fulani makiyaya da kashewa tare da yin garkuwa da mutanensu.
Majiyar ta ce fadan ya bazu zuwa garin Fikye inda aka ce an kashe mutane da dama.
Shugaban kungiyar Kutafawa na kasa, Emmanuel Ukwen, ya shaidawa manema labarai ta wayar tarho cewa an kashe mutane da dama daga bangarorin Kutafawa da Fulani makiyaya.
Shugaban karamar hukumar Ussa Abershi Musa ya yi murabus daga mukaminsa kan zargin da ake masa na cewa gwamnatin jihar ta gaza daukar mataki kan kisan gillar da Fulani makiyaya suka yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a Ussa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: