Sojojin Kasar Isra’ila Sun Kai Hare-hare Ta sama A Kudancin Lebanon da Zirin Gaza

0 88

Sojojin kasar Isra’ila sun kai hare-hare ta sama kan wasu sansanonin kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas a kudancin Lebanon da zirin Gaza.
Rundunar sojin ta ce hare-haren na mayar da martani ne ga harba makaman roka 34 da aka harba daga kasar Labanon zuwa arewacin Isra’ila a ranar Alhamis, wadanda ta dora alhakinsu kan kungiyar Hamas.
‘Yan bindiga a Gaza sun sake harba rokoki da dama bayan an fara kai hare-hare.
Hankali ya tashi kwanaki 2 da ‘yan sandan Isra’ila suka kai hari a masallacin al-Aqsa da ke birnin Kudus a farkon makon nan.
Hare-haren ya haifar da kazamin artabu da Falasdinawa a cikin masallacin, wanda shi ne wuri na uku mafi tsarki na Musulunci, ya kuma haifar da fushi a fadin yankin.
Hamas dai ba ta ce komai ba kan makaman rokar daga kasar Labanon, wanda shi ne hari mafi girma a cikin shekaru 17 da suka gabata.
Shugabanta Ismail Haniyeh, wanda ke ziyara a Beirut a wancan lokacin, ya ce Falasdinawa ba za su zauna da hannunsu ba” a yayin da Isra’ila ke kai wa hari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: