‘Yan bindiga sun sace wasu mata 13 da suka tafi bikia kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, saidai an sace sune a tsakanin Manini da Udawa.

Kamar yadda muka samu daga majiyar mu, lamarin dai ya faru ranar Alhamis da misalin karfe 12 na rana lokacin da ‘yan bindigar suka tare hanyar masu zuwa bikin.

Bayanai sun ce cikin matan harda wata uwa da ke shayarwa da kuma wata mata da ‘ya’yanta mata guda biyar kamar yadda BBCHausa ta ruwaito.

Haka kuma wani yaro dan shekara bakwai na cikin mutanen da aka sace.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: