Karin mutum 40 ne suka sake kamuwa da cutar korona a Najeriya

0 66

Ƙarin mutum 40 ne suka kamu da cutar korona ranar jiya Juma’a, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a ƙasar Najeriya.

Mutanen sun fito ne daga jiha huɗu. Sai dai babu wanda ya rasa ransa sakamakon cutar kamar yadda hukumar suka bayyana.

Jihohin su ne: Legas (36), Rivers (2), Gombe (1), Kano (1).

Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 167,732 ne suka harbu da cutar a Najeriya, yayin da 2,121 suka mutu a sanadiyyar cutar. Har yanzu dai wasu kasashen da dama na fama da cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: