Yan fashi da makami sun kai hari kan tawagar jami’an tsaro da ke rakiyar matafiya daga Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara.

‘Yan bindigar sun kona wata tankar man fetur a ayarin motoci don hana samar da mai a garin Dansadau, daya daga cikin garuruwan da’ yan ta’adda suka addaba a jihar Zamfara.

Mazauna Dansadau suna bukatar rakiyar tsaro don tafiya zuwa ko dawowa daga Gusau, don kare su daga hare-haren ‘yan bindiga.

Mazauna yankin sun ce tankar man na cikin motoci da dama da jami’an tsaro ke yi wa rakiya da motocin sulke zuwa Dansadau.

Wani mazaunin garin ya ce ‘yan fashin sun fito ne daga daji suka budewa tankar wuta, inda suka kona ta.

Wani basaraken gargajiya a masarautar Dansadau, Mustapha Umar, ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: