‘Yansanda sun kama mutane 13 a Jihar Katsina bisa zargin su da aikata laifukan kisa da garkuwa da mutane

0 89

A Kalla mutane 13 ne rundunar yan Sandan Jihar Katsina ta kama bisa zargin su, da aikata laifukan Kisa, Garkuwa da mutane da kuma satar Shanu a sassan Jihar.

Rundunar ta ce kamun yana daga cikin nasarorin da take samu a yaki da yan fashi da makami da kuma yan bindiga a Jihar.

Kakakin Rundunar SP Gambo Isah, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, a madadin Kwamishinan Yan sandan Jihar CP Sanusi Buba a Ofishin Hukumar dake Katsina.

A cewarsa, cikin mutanen da suka kama a ranar 16 ga watan Satumba, harda wani Mai Suna Surajo Mamman wanda aka fi sani da ‘‘Kutaku’’ a kyauyen Tulun Busawa wanda kuma yana daga cikin masu addabar sassan Jihar.

A lokacin binciken sun gano cewa Mutumin yana aiki ne karkashin Sani Muhidinge wani kasurgumin dan bindiga a Dajin Rugu.

Haka kuma mutumin ya fada musu cewa ya aikata hare-hare a Kananan hukumomin Dan Musa, Safana, Dutsinma da kuma Batsari.

Kazalika, ya ce bai san adadin mutanen da ya kashe ba cikin shekaru 15 da yayi yana aikata Kasuwan cinsa na fashi da makami.

Leave a Reply

%d bloggers like this: