Babban Jakada a ofishin jakadancin Najeriya dake Birnin New York na Amurka, Mr Benaoyagha Okoyen, ya shawarci yan Najeriya mazauna Amurka marasa muhallai da su koma gida Najeriya, inda yace ofishinsa a shirye yake wajen taimakawa wadanda ke san komawa.
Da yake jawabi a wani taro, akan cimma muradin cigaba, wanda ofishin jakadancin Najeriya na Birnin New York, ya dauki nauyi, Okoyen yace samar da gidaje ga yan Najeriya marasa muhalli, baya daga cikin ayyukan ofishin.
A cewarsa, babban abinda ofishinsa zai iya yi, a irin wannan yanayin shine bayar da shawarwari ga wadanda suke cikin matsin na rashin muhalli.
Babban Jakadan, na mayar da martani ne akan bukatar da mahalarta taron suka yi, suna jawo hankalinsa akan yadda ‘Yan Najeriya ke shan wahala akan titunan birnin New York da wasu garuruwan a Kasar Amurka.
Daya daga cikin mahalarta taron, Mr. Bernadine Uzor, ya nuna irin rayuwar kuncin da yan Najeriya ke ciki a Kasar Amurka.
Bernadine Uzor wanda shine jagoran Gidauniyar Asabe Shehu Yar’Adua, yace rashin muhalli babban kalubale ne ga ‘yan Najeriya.
Daga nan sai ya roki ofishin jakadancin daya taimaka wajen samar da gidaje ga marasa muhalli.