Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon tallafin abinci kashi na hudu a cikin watan Ramadana

0 137

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da rabon tallafin abinci kashi na hudu a kananan hukumomin 44 dake jihar a wannan wata na Ramadana.

Abba Kabir, ya kaddamar da rabon kayan tallafin ne a kamfanin sarrafa shinkafa na Tiamin Rice Mill dake kan titin Zaria a jihar ga masu karamin karfi da kuma mabukata.

Gwamnan ya gargadi masu aikin rabon kayan tallafin da su guji karkatar da kayayyakin.

Yace dukkanin wanda aka samu da karkatar da kayan tallafin zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Ya kara da cewa kayan tallafin sun kunshi buhun shinklafa masu nauyin kilogram 25 wadanda aka samar domin rabawa ga al’umma don rage musu radadi a wannan lokacin na Azumin Ramadana. Kazalika Abba Kabir, ya ce buhun shinkafa dubu 224 da dari 440 ne za a rabawa al’ummar gundumar yan majalisu uku dake fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: