Abubuwa 5 game da wasan Nigeriya da Tunusia

0 137

Nigeria zata kara da Tunisia a cigaba da kokarin kungiyar kwallon kafar Nigeria na shirin tunkarar wasannin yunkurin fitowa gasar Kofin Nahiyar Afrika da zata fara fafatawa a watan Nuwamba da kungiyar Sierra Leone

Kungiyar Nigeria ta Super Eagles karkashin mai horaswa Gernot Rohr zasu yi namijin kokari don ganin sun farfado daga rashin nasarar da suka yi a hannun zakarun nahiyar Afrika kasar Algeria da ci 1-0.

Nigeria vs Tunisia yadda abun yake;

Nigeria vs Tunisia sun gamu har sau 19 a wasannin sada zumunta da yunkurin fitowa gasar kofin Duniya da na Nahiyar Afrika da kuma AFCON.

Komai na Nigeria da Tunisia daya ne a tarihin gamuwarsu, babu wanda ya zarta wani. wannan wasan na yau shi ne zai dora daya a gaba.

Nigeria vs Tunisia suna da nasarori sau shida-shida sai kuma wasanni bakwai d aka tashi canjaras.

Yan wasan da ake sanya rai (wata kila) zasu fara takawa Nigeria kwallo sune:
Okoye, Ebuehi, Troost-Ekong, Balogun, Sanusi; Ayaji, Onyeka; Chukwueze, Iwobi, Kalu; Iheanacho

Yan wasan da ake sanya rai (wata kila) zasu fara takawa Tunusia kwallo sune:
Ben Cherifia; Kechrida, Bronn, Mariah, Maaloul; Slimane, Skhiri, Ben Mohamed; Rafia, Khazri, Khaoui.

Sai dai kuma kash wasanni uku da suka gabata tsakanin su Nigeria vs Tunisia ya kare ne babu wanda yayi nasara kan wani, don haka ne yau a kasar Austria wasannin zasu yi matukar daukar hankali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: