Wata sabuwa: Za’a yiwa mutane miliyan 9 gwajin Korona a China

0 205

Sama da mutane miliyan 9 ne dake birnin Qingdao na kasar Sin ake shirin yiwa gwajin cutar corona.

Hukumomin lafiya sun rawaito cewa kusan mutane 12 ne aka gano sun kamu da cutar a birnin cikin karshen makon da ya gabata, wanda galibi ke da alaka da wani asibiti.

Haka kuma sama da mutane 140,000 da galibinsu ma’aikatan kiwon lafiya ne akayi musu gwajin cutar tun bayan billar ta a karon farko.

A baya bayannan dai masu dauke da cutar a kasar, sun kasance wadanda suka shigo ne daga ketare, to sai dai lamarin na karkashin kulawa bisa tsauraran matakan da aka shimfida da suka hadar da dokar kulle da kuma killace kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: