Akalla Mutum 3 Ne Suka Mutu Yayin Arangama Tsakanin Sojoji Da Wasu Mayaka A Sudan

0 85

Akalla mutane uku ne suka mutu bayan sojojin Sudan da wasu mayaka sun yi arangama da muggan makamai a Khartoum babban birnin kasar, ana tsaka da shirin mika mulki ga farar hula.
Wani faifan bidiyo ya nuna wani jirgin saman farar hula yana ci da wuta a filin jiragen saman Khartoum. Kamfanin jiragen saman Saudiyya yace an kai hari kan daya daga cikin manyan jiragenta.
Dukkan bangarorin biyu sunce suna da iko da filin jiragen saman da sauran muhimman wurare. Sojoji sun ce jiragen yaki na kai farmaki kan sansanonin abokin adawa na kungiyar mayakan RSF.
Mutane na neman mafaka daga fadan kasancewar mazauna birnin ba suyi tsammanin fadan ba kuma ya rutsa da su akan hanya, inda aka rufe gajoji da tituna tare da kulle makarantu da dama.
Jakadan Amurka a kasar, John Godfre, yace ya tashi da jin karar harbin bindiga da na fada.
Ofishin jakadancin Rasha a kasar ya bayyana damuwa bisa kasuwar rikici inda ya bukaci a tsagaita wuta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: