Peter Obi Yasha Alwashin Babu Wanda Ya Isa Tursasa Shi Barin Najeriya

0 70

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya sha alwashin cewa babu wanda ya isa ya tursashi barin Najeriya.
Peter Obi, wanda a ‘yan kwanakinnan yayi zargin cewa yana fuskantar matsin tserewa daga kasarnan, yace ya tsaya tsayin daka wajen samar da sabuwar Najeriya.
Da yake jawabi a Onicha yayin gangamin yakin neman zaben dan takarar jam’iyyar Labour na mazabar Ogbaru ta dan majalisar wakilai ta tarayya, Afam Ogene, Peter Obi yace akwai barayi dayawa a kasarnan wadanda ke azabtar da talakawa.
Sai dai, ya jaddada cewa jam’iyyar Labour ta jajirce wajen kakkabe irin wadannan mutanen daga siyasar kasarnan.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra, wanda ya samu rakiyar wadanda suka samu nasarar zaben sanatoci na jam’iyyar Labour, Tony Nwoye da Oseloka Obaze, ya gayawa mutane cewa Afam Ogene yana da akidarsa ta gina sabuwar Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: