Al’ummar kasar Saliyo na kada kuri’a a babban zaben kasar bayan wani gangamin yakin neman zabe mai cike da tashin hankali.
A ranar Laraba, babbar jam’iyyar adawa ta yi zargin cewa ‘yan sanda sun harbe daya daga cikin magoya bayanta, lamarin da ‘yan sandan suka musanta.
Ana zargin magoya bayan manyan jam’iyyun biyu da kai wa juna hari.
Ana gudanar da wannan zabe ne bisa ga yanayin da tattalin arzikin kasar ke fama da shi, da tsadar rayuwa, da kuma damuwar hadin kan kasa.
Masu kada kuri’a na zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar dokoki da kansiloli a zaben kasar da ke yammacin Afirka karo na biyar tun bayan kawo karshen yakin basasa a shekara ta 2002. Rikicin da aka kwashe shekaru 11 ana yi ya janyo hasarar rayuka kimanin dubu 50 amma tun daga lokacin kasar na da al’adar gudanar da zabe cikin lumana, da ‘yanci da kuma sahihin zabe, a cewar shugabar kungiyar masu sa ido kan zaben kasar, Marcella Samba Sesay.