Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) ta bai wa kamfanin sadarwa na MTN izinin katse hanyar sadarwa ta Glo a kan bashin da ake bin sa.
NCC, a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun daraktan hulda da jama’a, Reuben Muoka, ta bayyana cewa kamfanin na MTN ya sanar da Globacom aikace-aikacen da MTN ya gabatar kuma an ba ta damar yin tsokaci tare da bayyana lamarin.
Hukumar ta ce, bayan nazarin aikace-aikacen da kuma yanayin da ke tattare da bashin, ta gano cewa Globacom ba ta da wasu muhimman dalilai na rashin biyan kudaden haɗin gwiwar.
NCC ta ce wannan katsewar za ta ci gaba da wanzuwa har sai an tabbatar da hakan.
Bincike ya nuna cewa kamfanin sadarwa na Globacom yana da abokan hulda miliyan 61 kuma kashi 27.8 cikin ɗari na jumillar masuy amfanin da layukan sadarwa.